An yi asarar miliyan 800 a kasuwar waya a Kano

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayoyin salula na samun karbuwa tsakanin al'umma

An tafka hasarar kusan naira miliyan 800 sakamakon gobarar da ta tashi a kasuwar wayoyin salula da ke unguwar Farm Center a Kano.

Wutar da ta tashi tun a daren ranar Talata ta shafe sa'o'i shida kafin a samu damar kashe ta a safiyar ranar Laraba.

Mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Sulaiman Abba Sharada ne ya shaida wa BBC wannan adadin na dukiyar da aka tafka sakamakon gobarar.

Ya ce "Runfunar katako kusan 500 sun kone, sannan shaguna kusan 50 suma gobarar ta lalata su."

Dubban mutane ne ke hada-hada a kasuwar ta waya ta Kano, wacce take daya daga manyan kasuwnnin waya a Nigeria.