Sojin Nigeria sun musanta zargin kafa gwamnati

Sojojin Nigeria ya yin wani taro.
Image caption Rundunar sojin kasar sun ce sam babu ruwan su a cikin wannan batu, zargi ne kawai da son tada zaune tsaye.

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata zargin da ta ce ana yi na yunkurin kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar a karkashin jagorancin sojoji matukar jam'iyar PDP mai mulki ba ta yi nasara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a watan Fabrairu ba.

Rundunar ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata.

Kanal Sani Usman Kukasheka, shi ne sabon kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, kuma ya ce ana yada wannan jita-jitar ne domin kawo sabani tsakanin sojojin kasar.

Kukasheka ya ce "babu kanshin gaskiya a wannan magana, ba ayi ta ba, ba za kuma a yi ta ba, sam ma ba za ta yiwu ba."

Kazalika ya musanta batun da ake yi na cewa shugaban hafsan sojin Nigeria ya yi taro da manyan hafsoshin sojin kasar, kuma ya bukaci a marawa wata jam'iyyar baya.