An fara aiken jirgi mara matuki da kaya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Irin yadda ake aiken jirgi marar matuki kai kaya ga jama'a

Babban kamfanin sayar da kayayyaki ta Intanet, na China, Alibaba, ya fara gwajin aika kayan da yake sayarwa ga jama'a ta hanyar amafani da karamin jirgi mara matuki.

Kamfanin ya ce, zai yi gwajin ne na kwanaki uku, kuma zai takaita tsakanin yankunan da jirgin zai iya zuwa cikin sa'a daya don kai kayayyakin, a Beijin da Shangai da Guanzhou.

Kamfanin ya bayyana a shafinsa na tallace-tallace a intanet cewa yana ganin fasahar za ta iya sa aikewa da kayayyakinsa cikin sauri.

Kamfanin Amazon da Google da kuma na aika wasiku UPS na daga kamfanonin da su ma suke gwajin amfani da jirgin maras matuki, wajen aika wa jama'a kayayyaki.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai kamfanin,Jack Ma, ya ce yana son zuwa 2025 mutane biliyan biyu a duniya su rika amfana da shirin

Alibaba na amfani da kananan jiragen wajen aikawa da wani ganyen shayi na citta, wanda hakan ya taimaka wajen takaita nauyin kayan zuwa gramme 340.

Ana daure kwalin da ke dauke da ganyen shayin ne a tsakanin kafafuwan jirgin.

Duk da cewa an takaita gwajin tsakanin mutane 450, amma reshen kamfanin na Alibaba na China Taobao, wanda ke wannan gwaji, yana aikawa da kayayyaki ne na gaske ga mutanen gaske.

Kuma wannan wani mataki ne na cigaba, idan aka kwatanta shi da takwaransa na Yammacin duniya Amazon, kamar yadda Paul Bischoff na BBC ya ce.

Sai dai kuma kamfanin na Alibaba bai bayar da bayanai kan yadda zai tabbatar amfani da wannan fasaha bai haifar da hadari ba.