An yi yunkurin fasa kurkuku a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Ghana John Mahama

Rahotanni daga Ghana na cewa wasu fursunoni sun yi yunkurin fasa wani gidan yari da ake tsare da su a Kumasi, birni na biyu mafi girma a kasar.

Rahotannin sun ce fursunonin sun tayar da wuta a daya daga cikin dakunan da ake tsare da su, sannan suka farma jami'an gidan yarin.

Jami'an 'yan sanda sun yi harbe-harbe tare da amfani da hayaki mai sa hawaye akan fursunonin.

Ko da ike an samu rahotannin mutuwa a lamarin, amma ba a fayyace ko daga wana bangare aka yi rashin ba, da kuma yawan wadanda suka samu raunuka.