2015: Ana taron majalisar kasa a Najeriya

Image caption Tsofaffin shugabannin kasar na cikin mahalarta taron.

Majalisar kasa ta Nigeria na can tana wani taro a karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan.

Ana yin taron ne a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Kawo yanzu babu wani bayani kan ajandar taron, amma jama'a da dama na ganin za a tattauna a kan batun zaben shugaban kasar da za ayi .

Wannan taro ya zo ne a yayin da wasu ke kiran a daga lokacin yin zaben, wasu kuwa ke nuna adawarsu da duk wani mataki na sauya lokacin daga 14 ga watan nan da muke ciki.

Wakilinmu a fadar shugaban Najeriyar ya ce kusan dukkanin gwamnonin jihohin kasar da tsofaffin shugabannin kasar -- ciki kuwa har dan takarar babbar jam'iyyar hamayya Janar Muhammad Buhari -- suna halartar wannan taro.

An dai shirya shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Attahiru Jega, zai gabatar da jawabi ga taron.