2015: Ban yarda a jinkirta zabe ba - IBB

Image caption Wasu daga cikin tsofaffin shugabannin kasa a Nigeria

Tsohon shugaban mulkin sojin Nigeria, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce bai kamata mutane su dinga tunanin a dage zabukan kasar da ke tafe nan da 'yan kwanaki ba.

A hirarsa da BBC, Janar Babangida ya ce tun da hukumar zabe ta ce ta shirya, to ya kamata a ba ta dama domin ta gudanar da aikinta na tabbatar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Babangida ya ce "Hukumar zabe ta tabbatar mana ta shirya domin gudanar da wannan zaben domin haka babu batun dage zabe".

"Ina kira ga mutane su san cewa zabe zai zo ya wuce domin haka mutane su zauna lafiya ka da su tayar da hankali," in ji tsohon shugaban kasar.

Wasu daga cikin 'yan Nigeria suna kira a jinkirta zaben saboda batun bai wa INEC karin lokacin domin ta samu damar rarraba katunan zabe na din-din-din.

A ranar 14 ga wannan watan aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki a fadin Nigeria, sai kuma na gwamnoni da 'yan majalisar dokokin jihohi a ranar 28 ga watan Fabarairu.