Nato: Rasha ta karya dokar kasa da kasa

Hakkin mallakar hoto nato.int
Image caption NATO za ta sansani a gabashin Turai

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya ce kasar Rasha na ci gaba da karya dokar kasa da kasa a Ukraine.

Yana magana ne yayinda ministocin tsaro na kungiyar ke hallara a birnin Brussels don tattauna yadda za a kara yawan dakarun kawance na hadin guiwar tsaro, tun bayan da aka kawo karshen yakin cacar baka.

Mr Stoltenberg ya tabbatar da cewa za a tanadi dakaru dubu biyar a gabashin Turai.

Shi kuwa ministar harkokin tsaron Jamus, Ursula von der Leyen, ta ce yunkuri ne mai matukar muhimmanci.

Rikicin da ake yi a Ukraine ya janyo an kakabawa kasar Rasha takunkumi bisa rawar da ake zarginta na taimaka wa 'yan aware.