Shugabar kamfanin Sony ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kutsen ya bayyana wasu sakonnin sirri da shugabar ta aika wa wasu

Daya daga cikin manyan shugabannin kamfanin shirya fina finai na Sony, Amy Pascal ta yi murabus sakamakon kutsen satar bayanai da aka yi wa kamfanin wanda ya bayyana wasu sakonninta na sirri.

Cikin sakonnin nata da suka bayyana ga jama'a, har da wanda ta bai wa wani mai shirya fina finai labarin irin halayyar shugaba Obama na Amurka wajen kallon fim, abinda ta yi da lafuzza marasa dadi.

Mis Pascal zata bude wani kamfanin shirya fina finan na daban da zai fara aiki a watan Mayun wanan shekara.

Ta bai wa jama'a hakuri bisa sakonnin nata da suka fita bainar jama'a sakamakon kutsen.

A cikin watan daya gabata, kamfanin na Sony ya yi Allah wadai da kutsen, wanda ya sa har kamfanin ya dakatar da nuna fim din 'The Interview' daga farko.

Mis Pascal ta ce "kusan duk kan lokacin da na yi ina aiki, a kamfanin Sony ne nayi, kuma na samu kwarin gwiwa sosai, har gashi ina neman fara aiki a sabon wuri".

A zaman wani bangare na yarjejeniyar tafiyar ta, kamfanin Sony zai samar da kudin tafiyar da sabon kamfanin nata na tswon shekaru 4, yayin da zai zamo mai iko da rarraba fina finan da zata rika yi.

Kamfanin Sony bai sanar da sunan wanda zai maye gurbinta ba, inda yanzu Michael Lynton ne kadai zai ci gaba da jan ragamar kamfanin.