Mutum ya kashe Kadan da ya cinye matarsa

Hakkin mallakar hoto MOSES BIKALA
Image caption Kadan ya kai mita hudu kuma nauyinsa ya kai kilo 600

Watanni hudu da suka wuce ne Kada ya cinye Demeteriya Nabire lokacin da ta je diban ruwa a rafi, sai dai bayan kadan ya dawo wurin ya tarar da mijin matar na jiran daukar fansa.

Demeteriya Nabire na bakin rafin ne tare da wasu mata na kauyensu suna diban ruwa a rafin Kyoga a kasar Uganda, a lokacin da kadan ya cafke ta ya kuma janye ta cikin ruwa tun daga sannan ba a kara ganinta ba.

Mijin Matar, Mubarak Batambuze ya dimauce domin matar tasa na da juna biyu a lokacin da ta mutu.

To amma a watan daya gabata sai ya samu labarin cewa Kadan ya dawo rafin.

"Wani ne ya kira ni ya ce Mubarak ina so in baka wani labari, Kadan da ya yi ajalin matarka ya dawo ga shi nan muna kallonsa."

Don haka sai Mubarak ya je wajen makerin da ke kauyensu.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ya ce "Na yi masa bayanin cewa ina so in yi fada ne da wata dabba da ta kashe matata da dana, ina matukar so in dauki fansa. Sai na ce makerin ya kera mini mashin da zan iya amfani da shi wajen kashe dabbar."

"Makerin ya caje ni £3.20 sannan ya kera mini mashin" wannan ba karamin kudi ba ne a wajen Mubarak, amma bai damu ba saboda yana son ya dauki fansa kan abin da ya kashe masa iyali.

Sai ya dauki mashinsa ya nufi bakin rafi inda ya samu Kadan, sai dai abokansa sun nuna fargabarsu cewa kada Kadan shi ma ya cinye shi, suka roke shi da kada ya yi fada da shi, domin yin amfani da mashi kadai ba zai kashe Kadan ba.

Ya dauki Mubarak sa'a daya da rabi kafin shi da abokansa su kashe Kadan, Mubarak na jifa da mashi su kuma suna taimaka masa da jifan dabbar da duwatsu.

Mutanen kauyen sun yi ta jinjina wa Mubarak da abokansa ganin girman Kadan da suka kashe.