Boko Haram ta kai hari a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan shi ne karon farko da aka kai hari a Jamhuriyar Nijar

Rahotanni daga garin Bosso na Jamhuriyar Nijar na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a ranar Juma'a.

Garin dai yana kan iyakar Najeriya ne da Jamhuriyar ta Nijar.

BBC ta tabbatar da cewa sojojin Nijar da na Chadi sun fafataki 'yan kungiyar ta Boko Haram, bayan 'yan kungiyar sun shiga Nijar ta garin Malam Fatori da ke Najeriya.

Wasu rahotannin na cewa sojojin Nijar biyar sun jikkata a fafatawar.

Kazalika, wasu 'yan kungiyar sun yi yunkurin shiga Nijar din ta garin Damasak na jihar Yobe da ke Nigeria, ko da yake a can din ma, sojin Nijar sun tarwatsa 'yan kungiyar.

Wannan dai shi ne karon farko da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke kai hari a Jamhuriyar Nijar.

A kwanakin baya shugaban kungiyar ya yi barazanar kai wa kasar hari.