Google zai sabunta tabaran komai-da-ruwanka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Batun amfani da tabaran na Google Glass dai ya jawo cece-kuce a baya

Kamfanin Google zai sake fara aikin kirkiro tabaran komai- da-ruwanka mai gani har hanji, da ake kira Google Glass, inji jaridar New York Times

A watan Janairu aka dakatar da sayar da tabaran, kuma ana ganin an tsayar da aikin kera samfurinsa.

Yanzu dai aikin kirkiro tabaran ya koma hannun tsohon mai zayyana na kamfanin Apple, Tony Fadell, wanda ya sake tsarin aikin kirkirar.

Jaridar Times din ta ruwaito cewa yanzu za a yi aikin kera tabaran ne a cikin kamfanin na Google, kuma sai an kammala shi za a fito da shi.

Lokacin da aka fara bayyana tabaran na Google Glass a 2011, ya yi tasiri sosai a 2012.

A lokacin kamfanin ya bai wa masu wasan saukar lema da masu wasan keke su jarraba tabaran.

Jaridar ta ce cece-kucen da aikin kirkiro tabaran ya haifar ta tilasta wa wasu daga manyan kwararrun masu aikin barin kamfanin.

Yanzu dai aikin kera tabaran na Google Glass ya koma hannun Mr Fadell, wanda ya taimaka wajen kirkiro iPod da sauran na'urorin kamfanin Apple.

A shekarar da ta wuce ne Mr Fadell ya zama ma'aikacin Google bayan da kamfanin ya saye kamfanin da yake yi wa aiki, Nest.