An yi bikin bai wa Sarki Sanusi sandar mulki

Image caption Mai martaba Sarki Sanusi na biyu

Gwamnatin jihar Kano ta kamalla bai wa Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II sandar girma a wani buki da aka yi yau Asabar.

Tun farko dai wakilin BBC a Kano Yusuf Yakasai ya ce fadar Kano ta dau harami domin bikin nadin, kuma gwamnatin jiha ta gina wani sabon dakin taro a gidan gwamnati wanda a ciki aka yi bikin nadin.

Wakilin na BBC ya kuma ce otal-otal na Kano sun cika da baki daga sassa daban-daban na duniya.

An kuma yi wa fadar Sarki gyare-gayare na musamman domin bikin.

A ranar 8 ga watan Yuni aka nada Alhaji Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan rasuwar Sarki Ado Bayero a ranar 6 ga watan Yuni.

Wannan dai shi ne karo na farko da za a bayar da sanda ga sarki a Kano tun shekarar 1963.