An daina bayar da karamin sakamako a jami'a

Image caption Mallam Ibrahim Shekarau ministan ilimi na Najeriya

Hukumar kula da jami'o'in Najeriya, NUC, ta ce ta soke bayar da sakamakon karatun jami'a na ba-yabo-ba-fallasa wato pass.

A farkon makon nan aka ruwaito shugaban Jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, Farfesa Abdullahi Zuru, ya bayyana hakan lokacin bikin karbar sabbin dalibai a jami'ar.

Matakin na nufin duk dalibin da ya ci kasa da maki 45 maimakon maki 40 da aka saba bayarwa a darasi, ba zai samu fita daga jami'ar ba.

To sai dai wasu malaman jami'a na ganin akwai mataka share fage da ya kamata hukumar ta dauka kafin ta kai ga sokewar.

Mallam Abdullahi Umar Alhassan na jami'ar ta Usman Danfodiyo, ya ce kamat ya yi hukuma ta mayar da hankali wajen gyara manhajar karantar da dalibai, ta zamo ta dace da kalubalen zamani.