Majalisar dinkin duniya ta gargadi Mali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon

Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya, ya bukaci dakarun gwamnati da na 'yan tawaye a arewacin Mali da su koma kan teburin sasantawa ba tare da wani jinkiri ba, ko ya sa musu tukunkumi.

A watan da ya gabata, an samu karin fadace-fadace a arewacin kasar inda, 'yan gwagwarmayar Islama da mayakan Abzinawa 'yan aware ke fafutukar kama iko tun lokacin da aka rasa tartibiyar gwamnati bayan juyin mulkin da aka yi a Malin a 2012.

Majalisar dinkin duniya da kasar Algeria da ke karbar bakuncin zaman tattaunawar, suna fargabar cewa rikicin zai iya kawo nakasu ga shirin zaman lafiyar.