Boko Haram: kasashe 5 za su samar da dakaru 8750

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Najeriya da Chadi da Nijar da Kamaru da Benin za su hada karfi domin yakar Boko Haram

Kasashen Najeriya da Benin da Chadi da Kamaru da Nijar za su samar da dakaru 8750 domin hada karfi wajen yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.

Kasashen sun amince da hakan ne a karshen wani taron kwanaki uku da suka gudanar a Kamaru.

Daga cikin dakarun karo-karon, da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma fararen hula, kasar Chadi da Najeriya za su samar da 3500 kowaccensu, a yayin da kasar Kamaru da jumhuriyar Nijar kowace za ta samar da dakaru 750.

Kasar jamhoriyar Benin za ta samar da dakaru 250, yayin da Ndjamena na kasar Chadi zai kasance wurin da za a kafa cibiyar wannan runduna.

Wannan na zuwa ne bayan da farkon wannan wata kungiyar tarrayar Afirka ta sanar da tsarin samar da dakaru dubu bakwai da dari biyar domin yakar yan kungiyar ta Boko Haram.