Ukraine: Putin ya gana da Hollande da Markel

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rasha ta ce tattaunawar za ta yi fa'ida

Shugabannin Faransa da Jamus sun gana da Vladimir Putin na Rasha a game da rikicin gabashin Ukraine.

Gwamnatin Kremlin ta bayyana tattaunawar a matsayin mai fa'ida da za ta iya kawo karshen rikicin.

Ana ganin tattaunawar da shugabannin suka shafe sama da sa'o'i 4 suna yi, wani babban mataki ne na gaske na warware rikicin na Ukraine.

Kakakin shugaban Rasha, Dmitry Peskov ya ce bisa shawarorin da Faransa da Jamus su ka bayar, ana aiki akan wata yarjejeniya ta yiwuwar aiwatar da yarjejeniyar Minsk.

Mista Peskov ya ce shugabannin za su sake tattauna wa da shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ta wayar tarho a ranar Lahadi.