Ba a yi mana katsalandan ba, in ji INEC

Hukumar zaben Najeriya ta musanta zargin cewa an tilasta mata ne ta dage zaben kasar da aka shirya yi ranar Asabar zuwa ranar 28 ga watan Maris.

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne bisa la'akari da shawarar da hukumomin tsaro suka bata cewar ba za su samu damar bayar da cikakken tsaro ba a lokuttan zaben, muddin aka ce za a yi shi a ranar Asabar mai zuwa.

Hajiya Amina Zakari, babbar kwamishiniya a hukumar zaben, ta ce hukumar ba ita kadai ta ke aiki ba, tana aiki tare da wasu hukumomi ne, don haka wajibi ne ta saurari sauran abokan aikinta wajen yanke hukunci.

Ta ce dage zaben zai baiwa hukumomin tsaron dama su aika jami'an tsaron da za su tabbatar da gudanar da zaben lami lafiya.

Haka kuma ta ce sauran mutanen da ba su samu kadin zabe na-din-din-din ba yanzu za su samu katin kafin gudanar da zaben.

Karin bayani