Jordan na yi wa mayakan IS luguden wuta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin saman Jordan na yaki

Rundunar sojin sama ta kasar Jordan ta ce ta aiwatar da farmaki ta sama har sau hamsin da shidda a kan mayakan kungiyar IS a Syria cikin 'yan kwanakin da suka wuce.

Laftanar Janar Mansour al Jbour, ya ce Jordan ta tsananta farmakin ramuwar gayya a kan kisan gillar da masu da'awar jihadin suka yi wa matukin jirgin saman kasar da suka kama.

A cewarsa farmakin ya lalata cibiyoyin horaswa da na makamai da kuma maboyar mayakan.

Bugu da kari ya ce Jordan da kawancen hadakar kasashe da suke kai farmaki sun kashe mayakan IS fiye da dubu saba'in a makonni biyar da suka wuce.

Ya kara da cewa "Ana harar shugabannin kungiyar ne da kuma musamman jagoransu al-Baghdadi."