An kai harin kunar bakin wake a Nijar

Niger Violence
Image caption Wannan da ake kai harin kunar-bakin-wake a Nijar

Rahotanni daga garin Diffa na jamhuriyar Nijar na cewa wani bom ya tashi da wani dan kunar-bakin-wake a wata kasuwar tattasai da ke cikin garin.

Harin ya yi sanadiyar mutuwar dan kunar-bakin-waken tare da jikata mutane da dama.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da 'yan kungiyar boko haram ke matsa kaimin kai hare-hare a bakin iyakar Diffar da Najeriya.

A yanzu haka dai ministan tsaron kasar ta Nijar na jahar ta Diffa inda yake wata ziyarar aiki, bayan hari na farko da 'yan kungiyar ta boko haram din suka kai ranar Jumu'a; wanda ya yi sanadiyar mutuwar jami'an tsaron Nijar 4 da farar hula 1,da kuma yan boko haram din su 109.

Ana sa ran majalisar dokokin Nijer din za ta kada kuri'a a kan bukatar neman a tura dakarun kasar zuwa Najeriya domin yakar 'yan Boko Haram a ranar Litinin.

Karin bayani