Amurka ta ji takaicin jinkirta zaben Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption John Kerry ya ce suna sa ido a kan lamuran da ke faruwa a Nigeria

Amurka ta ce ta ji takaicin jinkirta ranar da za a gudanar da zaben shugaban Nigeria daga watan Fabarairu zuwa watan Maris.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry a wata sanarwa ya ce "Amurka ta yi matukar rashin jin dadin dage ranar zaben shugaban kasa daga 14 ga watan Fabarairu."

Hukumar zaben Nigeria- INEC ce ta sanarda karin makonni shida kafin gudanar da zabukan bayan tattaunar da ta yi da manyan hafsoshin tsaron kasar.

Mr Kerry ya jaddada cewa "Ba a lamunci duk wata katsalandan na siyasa ba a kan hukumar zabe."

Ya kara da cewar kasashen duniya suna sa ido a kan yadda gwamnatin Nigeria ke shirin gudanar da zabukan a nan gaba.

Batun tabarbarewar tsaro a yankin arewa maso gabashin Nigeria ne hujjar da jami'an tsaro suka bayar na bai wa INEC shawarar dage zaben.

Rikicin Boko Haram a arewacin kasar ya janyo mutuwar akalla mutane 13,000 cikin shekaru shida.