Ba mu karaya ba – Buhari

Janar Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto apc
Image caption Matakin dage zaben da hukumar INEC ta dauka bai yi wa jam'iyyar adawa ta APC dadi ba.

A Najeriya, dan takarar shugabancin kasar a karkashin Jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya ce dage zabukan kasar da aka yi shi ne na karshe da kundin tsarin mulkin kasar ya yarda da shi.

A martaninsa na farko tun bayan bayar da sanarwar dage zabukan a daren Asabar, Janar Buhari ya shaida wa taron manema labarai a Abuja cewa koda yake dage zaben bai yi musu dadi ba, wannan sam bai sa suka karaya ba.

Janar Buhari ya kara da cewa za su jajirce a yi zaben kamar yadda aka tsara, kuma idan har wa'adin da aka tsaida na 28 ga watan gobe domin gudanar da zabe ya cika, to gwamnati ba ta da hurumin sake daga zaben.

A cewarsa, idan gwamnati ta sake kawo wani dalili na daban, to kuwa jam'iyyarsa ba za ta amince da hakan ba, yana mai cewa idan kuma gwamnati ta kasa yi to ita ma sai dai ta sauka daga mulkin Nigeria, ko dai ta ba wa sojoji mulkin, ko kuma ta ce ita ta kwace mulkin babu ruwanta da Dimukradiyya su kuma 'yan kasar su suka san yadda za su yi da su.