China ta zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane

Wurin zartas da hukuncin kisa a China Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wurin zartas da hukuncin kisa a China

Hukumomin kasar China sun ce sun zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane biyar da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Mutanen sun hada da wani babban dan kasuwa da yake da alaka da tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gida a kasar ta China.

Liu Han shi ne shugaban wani babban kamfani mai zaman kan sa da ke yankin Sichuan.

Tun a watan Mayun shekarar 2014 ne aka tuhume shi da laifin kisan kai da makarkashiyar wasu miyagun laifuka.

An bayyana Mr Liu a matsayin abokin kasuwancin dan Mr Zhou Yongkang dan shugaban hukumar tsaron cikin gida ta kasar, wanda a baya shi ne shugaban jami'iyya a Sinchuan.

Karin bayani