Ba za a kara dage zabe ba - Dasuki

Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Dasuki shi ne na farko da ya soma batun a dage zabe a Nigeria

Mai bai wa shugaban Nigeria shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki ya ce ba za a kara jinkirta ranar zabe ba daga ranar 28 ga watan Maris da aka tsayar.

A cewarsa, cikin makonni shida masu zuwa za a murkushe ayyukan 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

A sakon da aike wa BBC Dasuki ya ce "Daga wurinmu ba za a kara neman bukatar a dage zaben ba."

A makonnin da suka wuce ne Mr. Dasuki ya shawarci hukumar zaben Nigeria- INEC ta dage zabe domin ta samu damar rarraba katin zabe na dun-dun-dun.

An soki shawarar da cewa katsalandan ne daga wajen jami'an tsaro a kan harkokin zaben kasar.

Ana kallon zaben a matsayin wanda zai yi zafi tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan na PDP da kuma Janar Muhammadu Buhari na APC.