Karuwar hare-hare kan ilimin mata

Image caption Malala na cikin matan da aka kai wa hari.

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-hare a kan ilmin mata na faruwa tare da karuwa a koyaushe.

Rahoton, wanda Ofishin kare hakkin Bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva ya fitar, ya lissafta hare-hare a kan makarantu a kasashe saba'in, a cikin shekaru biyar daga 2009 zuwa 2014.

Rahoton ya kara da cewa yawancin hare-haren ana kai su ne a kasashen da 'yan kungiyoyin da ke ikirarin kishin Islama ke kai wa cikinsu har da Afghanistan, Nigeria da kuma Somalia.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar hare haren suna iya yin makarkashiya ga kokarin kara samar da ilmi ga 'yan mata.