An yi wa wata 'yar Nepal fyade a India

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fyade da gungun mutane ke yi a Indiya ya zamo babbar matsala

'Yan sanda a kasar Indiya suna neman wasu mutane da suka yi wa wata 'yar Nepal fyade kana suka kashe ta.

An samu gawar matar wadda take da matsalar koyon karatu a yashe a makon jiya.

Iyalanta dai sun zargi 'yan sanda da rashin daukar mataki a lokacin da ta bace.

Kuma a ranar Lahadi ne masu zanga-zanga suka datse wata babbar hanya domin nuna fushinsu ga 'yan sanda.