'Yan bindiga sun sace mahaifin Joshua Dariye

Hakkin mallakar hoto plateau state govt
Image caption 'Yan bindigar su tara ne suka sace Mr. Dariye

Rahotanni daga jihar Filato a Nijeriya na cewa hukumomin tsaro sun baza komarsu domin bin sawun wasu ‘yan bindiga da suka sace mahaifin tsohon gwamnan jihar, Cif Joshua Dariye.

An dai sace Mista Defwang Dariye ne mai kimanin shekaru 80 da haihuwa a gidansa da ke kauyen Mushere a yankin Bokkos a karshen mako.

Hukumomi dai sun ce babu wanda ya jikkata ko ya rasa ransa a harbe-harben da ‘yan bindigar suka yi a yayin sace Mista Defwang Dariye.

Kuma kawo yanzu ba a san inda ‘yan bindigar suka kai shi ba, amma bayanai na cewa sun bukaci kudin fansa.

Sace mutane tare da yin garkuwa da su ba sabon abu ba ne a Nigeria, inda ko a bara ma aka sace mahaifiyar ministar kudin kasar, Dr. Ngozi Nkonjo-Iweala.

Haka kuma a jihar ta Filato ne aka taba sace mahaifin dan kwallon kasa da kasar nan Mikel Obi.