Sojojinmu ba su kashe 'yan makaranta ba — Assad

Shugaba Basharul Assad Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An dai shafe shekaru hudu ana yaki a kasar Syria.

Shugaba Basharul Assad na Syria ya kare matakin da gwamnatinsa da sojojin kasar suka dauka a shekaru hudu da aka yi ana zubar da jini a yakin da ake yi tsakanin dakarun 'yan a ware da masu kaifin kishin Islama.

A wata tattaunawa da BBC, shugaba Assad yace tun da fari gwamnatinsa ta dauki matakin kare fararen hula daga abin da ya kira yakin ta'addanci.

Shugaba Assad ya musanta cewa dakarun sojin Syria sun yiwa makarantu ruwan bama-bamai, da kuma amfani da makamai masu guba ko kuma yin amfani da ababen fashewa dan kashe fararen hula a kasar.

Haka kuma Basharul Assad ya ya ki amincewa da zargin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na cewa dakarun sojin Syria sun sha hana ma'aikatan agaji isa wasu yankuna domin kai tallafi ga wadanda mummunan yakin ya rutsa da su.

Haka kuma Shugaba Assad yace Washington ba ta tuntube shu game da kai harin hadin gwiwa dan murkeshe masu tada kayar baya na IS ba, amma yace a kaikaice Amurka na turo da sakwan hakan ta hanyar wasu kasashe kamar Iraqi.