Amurka za ta aike wa Ukraine makamai

Shugaban Amurka Barack Obama da Angela Merkel ta Jamus Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama da Angela Merkel ta Jamus

Shugaban Amurka Barack Obama ya ce Amurka na yin nazari kan zabin da kasarsa ke da shi na aikewa da kasar Ukraine gudumawar makamai .

Ya ce zata yi hakan ne muddin yunkurin sasantawa ta hanyar diplomasiyya ya gagara kawo karshen tashin hankali a gabashin kasar.

Bayan tattaunawarsu da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta, Mr Obama ya kuma ce kasar Rashar ta sabawa duk wata yarjejeniya da aka kulla a Minsk.

Shugaba Obama na fuksnatr matsin lamba daga manyan jami'an gwamnatin Amurka na ya samar da makaman, duk cewa Ms Merkel na nuna adawa da batun.

Kasar Rashar dai ta musanta zargin aike wa da 'yan tawayen gabashin Ukraine karin dakaru da kuma makamai.

Dakarun gwamnatin ta Ukraine sun ce sojojinta akalla bakwai ne aka hallaka a fadan da ake gwabzawa cikin sa'oi 24 da suka gabata.