PDP na sayen katin zaben mutane — APC

Janar Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Muhammadu Buhari

Babbar jam'iyyar adawa ta APC a Najeriya ta zargi jam'iyyar PDP mai mulki da fara sayen katunan masu shirin jefa kuri'a a zaben shekara ta 2015 a kasar.

Jam'iyyar ta ce tuni ta kai koken ta ga hukumar zabe a kan yunkurin da ta ce PDPn na yi na sayen katin masu kada kuri'a a wasu sassan kasar.

Sai dai jam'iyyar PDP ta ce zargin da jam'iyar APC ta yi ba shi da tushe ballantana makama.

Ta kara da cewa ba zai yiwu ta sayi katunan zaben ba domin kuwa ko ta saya ba za su yi mata amfani ba ganin matakan da hukumarzabe ta dauka na kare su.

APC ta ce jam'iyyar PDP na karbar katin a matsayin jingina, kafin su bayar da rance ga mata da kuma sauran jama'a.

Wasu mutane da BBC ta tuntuba a Nijeriyar, sun bayyana cewar lallai wasu wakilai na jam'iyyar ta PDP sun nemi sayen katunansu, amma kuma a cewar su, ba su sayar da 'yancinsu ba.

Karin bayani