NEMA ta yi zargin ana fyade a sansanonin gudun hijira

'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan gudun hijirar rikicin Boko Haram

Jami'an Najeriya sun ce za su binciki zarge-zargen fyade da fataucin yara da sauran ayyukan cin zarafi a sansanonin 'yan gudun hijirar rikice-rikicen Boko Haram.

A wani rahoto da cibiyar bincike a aikin jarida ta Najeriya ta fitar, ta ce ta na zargin cewa jami'an da aka wakilta don su kare 'yan gudun hijirar na daga cikin ma su aikata cin zarafin.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar, NEMA, ta yi alkawarin kaddamar da bincike.

A cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, kimanin mutane miliyan uku da dubu dari biyu ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Arewa maso gabashin kasar.