Dakarun Niger sun kashe 'yan Boko Haram 300

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nijar ta amince ta tura sojojinta kasasehn Najeriya, Chadi da Kamaru don yakar Boko Haram

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun ce sojojin kasar sun kashe 'yan Boko Haram a artabun da suka yi a makon jiya.

Ministan tsaron kasar, Mahamadou Karidjo ne ya shaida wa BBC haka, a lokacin da yake tsokaci game da amincewa a tura sojin kasar domin yakar Boko Haram.

Karidjo ya ce ".....Harin da suka kai mana mun kashe yafi 300 da wani abu, amma ranar nan mun ce 109, ke nan ba wani tsoro za su bamu ba."

Inda ya kara da cewa kasar a shirye ta ke ta murkushe duk wani dan Boko Haram da ya kara sa kafa a cikinta.

A makon da ya gabata ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka fara kai hare-hare kasar ta Nijar.

Lamarin da ya jefa mazauna jihar Diffa cikin fargaba, inda har wasu suka fara barin yankin.