Gwamnatin Nijar za ta saki bayanan yaki da Boko Haram

Askarawan Nijar Hakkin mallakar hoto none

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce a shirye suke su ba 'yan jarida hadin kai ta hanyar ba su cikakkun bayanai game da abubuwan da ke faruwa a yankin jahar Difa.

Hasali ma za a kafa wani kwamiti da zai kunshi 'yan jarida da shugabannin sashen hulda da jama'a na rundunonin soja domin samar wa yan jaridar da bayanai a kai a kai.

An cimma wannan matsayin ne sakamakon wani taro da firayim ministan kasar ta Nijar Briji Rafini ya yi da yan jarida,taron da ya samu halartar ministocin tsaro da na yada labarai.

Ministan watsa labarai na kasar, ya ce Yahuza Sadisu Madobi, ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin kaucewa kamfar labarai.