Za mu sanya ido kan gwamnati — Obasanjo

Chief Olusegun Obasanjo Hakkin mallakar hoto
Image caption Chief Olusegun Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce 'yan kasar za su zura ido su ga ko za a samu sauyi a yanayin tsaron kasar cikin makonni shida da za a gudanar da zabukan kasar.

A wata hira da BBC, Chief Obasanjo ya kuma kawar da yiwuwar kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar, yana mai jaddada cewa yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Mista Obasanjo ya ce idan ya koma Nijeriya daga kasar Jamus, zai yi nazarin sababbin matakan da gwamnatin ta dauka wadanda take ganin za su ba ta damar inganta tsaro cikin makonni shida, abin da ba su yi ba cikin shekarun da suka wuce.

A cewarsa, bayan hakan ne zai yanke shawara kan ko zai yi tsokaci game da batun ko kuwa ba zai ce komai ba.

Karin bayani