Syria na samun bayanai daga Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Miliyoyin 'yan Syria ne ke gudun hijira a kasashen waje

Shugaban Syria, Bashar Al-Assad, ya ce gwamnatinsa na samun bayanai daga Amurka game da yakar masu da'awar gwagwarmayar Musulunci.

A wata hira da BBC, Assad ya ce babu wani hadin kai na kai tsaye da kawancen da Amurka ke jagoranta tun lokacin da aka soma kai hare-hare da jiragen yaki a cikin watan Satumba, to amma ana isar da sakonni ta hannun wata kafa ta daban kamar kasar Iraqi.

Shugaba Assad ya musanta cewa sojojinsa sun yi amfani da wasu miyagun bama-bamai barkatai a yankunan da 'yan tawaye ke rike da su a yakin da aka kwashe shekaru hudu ana yi a kasar.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam sun dage cewa dakarun gwamnatin ne kawai suke da jirage masu saukar ungulu wadanda da su ake harba bama-baman.

Mista Assad ya ce ba zai dauki nauyin bala'in da ake fuskanta a sassan kasar ba, biyo bayan yakin da ake yi a kasar.