Kotu ta haramta kungiyar Sharia4Belgium

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotun ta wanke wani mutum guda daga tuhuma kan ta'addanci

Wata Kotu a Belgium ta yanke hukuncin cewa wata kungiyar da ke kiran kanta Sharia4Belgium da cewa kungiyar 'yan ta'adda ce wadda ke samar wa mayaka masu jihadi na kasar Syria da wasu wurare makamai.

Alkalan sun ce ana zargin shugaban kungiyar, Fouad Belkacem, da jan ra'ayin matasan kasashen Turai da su daura damarar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

An dai yanke masa hukuncin shekaru 12 a gidan kaso.

Haka kuma an samun baki dayan mutane 45 da aka gurfanar da laifukan da suka shafi ta'addanci, inda aka yanke musu hukuncin shekaru 13 zuwa 15.

Sai dai mutane takwas ne kadai cikin wadanda aka yankewa hukunci ke kotun, yayin da wasu kuma ana tsammanin suna Syria ko ma sun mutu.

Shari'ar dai ita ce ake kallo mafi girma kan yaki da ta'addanci a Turai a cikin shekarun baya-bayan nan.