Boko Haram ta kai wa dakarun Chadi hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Chadi na yaki da Boko Haram a Nigeria

Mayakan Boko Haram sun kai wa dakarun Chadi hari a Gamborou ranar Laraba da asuba amma an kashe wasu daga cikinsu, sannan aka kama wasu 'yan Boko Haram din.

Wani mazaunin Gamborou ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun kai harin ne kusan karfe hudu na asuba, sai dai bisa dukkan alamu ba su yi nasara ba.

Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa, "Mayakan Boko Haram sun kawo mana harin ba zat a amma sun kwashi kashinsu a hannu."

Bayanai sun ce an kashe wasu 'yan Boko Haram sannan an kwace wasu daga cikin motocinsu na yaki.

A makon jiya ne Nigeria da Chadi da Kamaru da Niger da kuma Benin suka amince su kafa runduna mai dakaru 8,700 domin yakar Boko Haram.

Rikicin Boko Haram a Nigeria ya janyo mutuwar mutane fiye da 13,000 a cikin shekaru shida.