Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba

Image caption A yanzu darajar naira ta yi matukar faduwa

Darajar takardar kudin Nigeria watau Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba a tarihi saboda ta koma sama da Naira 200 a kan kowacce dalar Amurka daya.

Masu sharhi na ganin hakan ba zai rasa nasaba da dage manyan zabukan kasar da aka yi zuwa makonnin shida ba.

Gwamnatin Nigeria na kashe makudan kudade domin maido da darajar takardar kudin, amma faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya na yi wa hakan tarnaki.

A watan Nuwamban bara ne babban bankin kasar ya karya darajar naira da kashi goma sha takwas cikin dari sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

A hukumance, ana musayar kowacce dalar Amurka da naira 160 zuwa 176; amma ba a iya samun wannan musayar a cikin kasar.