Za mu kare dimokradiyya - Sojin Nigeria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sojin Nigeria sun ce ba za su yi katsalandan a harkokin dimokradiyya ba

Rundunar tsaron Nigeria ta jaddada cewa za ta yi iyaka kokarinta domin kare dimokradiyyar kasar a daidai lokacin lamura suka kara zafi kan zabukan kasar da aka daga.

Sanarwar da kakakinta, Manjo Janar Chris Olukolade ya fitar, ta ce sojojin Nigeria masu biyayya ne ga kundin tsarin mulkin kasar domin tabbatar da an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'umma.

A cewar Manjo Janar Olukolade, sojoji za su tsaya a kan huruminsu na kwararru kuma ba za su tsoma baki a kan abubuwan da suka shafi siyasa ba.

Wannan sanarwar na zuwa bayan da hukumar zaben Nigeria INEC ta sanar da jinkirta zabukan kasar bisa abin da ta ce shawarar da jami'an tsaron kasar suka ba ta.