Ba za a fasa zaben Nigeria ba - Jonathan

Shugaba Jonathan na Nijeriya Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Shugaba Jonathan na Nijeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce babu makawa za a gudanar da zabe a kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada kuma za a rantsar da gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

A wata hira da manema labarai ranar Laraba, Mr Jonathan ya ce jam'an tsaro da suka bai wa hukumar zabe shawarar dage zaben ba su tuntube shi ba.

Shugaban ya kuma musanta cewa yana shisshigi ga ayyukan hukumar zabe, yana mai cewa hukumar zaben na aikinta bisa tanadin kundin tsarin mulki.

Zan yi muku albishin kan 'yan matan Chibok

Ya ce babu kanshin gaskiya a game da zargin cewa gwamnati na matsin lamba wajen ganin ya sauke shugaban hukumar zaben, yana mai cewa ko kadan ba shi da wannan manufa.

Sai dai a game da batun dage zaben shugaba Jonathan yace ba batun tsaro ba ne kadai, akwai wasu dalilai ciki har da batun bada katin dundundun na kada kuri'a wanda ya ce a wasu jihohi ba a gama rabawa jama'a ba.

Jonathan ya ce alamu na nuna za a sami nasara nan ba da dadewa a kan Boko Haram musamman idan aka yi la'akari da hadin kan da Najeriya ta ke samu daga kasashe makwabta.

Ya kara da cewa cikin makonni kadan za a ji wani albishiri game da 'yan matan Chibok da ake kokarin ceto wa daga kungiyar Boko Haram.