Obasanjo ya bukaci 'yan Nigeria su zabi Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obasanjo ya ce Buhari yana da cikakkiyar kwarewa

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan kasar su zabi dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, a zaben 2015.

Obasajo ya bayyana goyon bayansa ga Janar Buhari ne a lokacin da ya kaddamar da littafinsa mai suna "My Watch" a birnin Nairobi na kasar Kenya.

A cikin littafin, Mr Obasanjo ya soki shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki.

A hirar da ya yi da jaridar Financial Times bayan kaddamar da littafin, Mr Obasanjo ya ce, "Idan Buhari ya ci zabe zai gudanar da mulki na daban, ba irin wanda ya yi ba lokacin yana mulkin soji. Shi mutum ne mai hikima. Yana da ilimi, yana da kwarewa. Don haka me ya sa ba zan goyi bayansa ba?"

Ya kara da cewa yana fatan shugaba Jonathan ba so yake ya tarwatsa kasar ba game da batun dage zabe.