'Yan gudun hijira 200 sun nutse a kogi

Hakkin mallakar hoto AFP Getty Images
Image caption Hukumar ta ce 'yan gudun hijirar sun mutu ne bayan jiragen ruwa sun nutse

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da 'yan gudun hijira 200 ne suka nutse a lokacin da suke yunkurin haura wa ta kogin Bahar Rum a 'yan kwanakin nan.

Hukumar ta bayyana haka ne bayan ta gana da wasu da suka tsira daga cikin kogin bayan jami'an kula da tekun Italiya sun tsamo su.

Sun kara da cewa 'yan gudun hijira da dama sun hallaka bayan igiyar ruwa ta yi awon-gaba da su lokacin da suka shiga jiragen ruwa daga kasar Libya.

A watan Nuwamba ne kasar ta Italiya ta kammala aikin ceto 'yan gudun hijrar da ta kwashe shekara guda tana yi.

Sai dai hukumar 'yan gudun hijirar ta yi gargadin cewa matakin zai sanya a samu karuwar 'yan gudun hijirar da ke mutuwa.