An kashe mutane 6 a babbar kasuwar Biu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira ne ke zaune a garin Biu

Wata 'yar kunar bakin wake ta tarwatsa kan ta a wata kasuwa dake makare da jama'a a garin Biu dake jihar Borno arewa maso gabashin Najeriya.

Mutane akalla shida ne aka bayyana sun rasa rayukansu yayinda da dama suka samu raunuka a wani harin.

Wasu 'yan banga dake yankin ne suka cafke sauran 'yan kunar bakin waken biyu da dukkansu 'yan mata ne--da suka gaza tada bam din dake daure a jikinsu.

Mayakan kungiyar Boko Haram na amfani da yaran mata da basu wuce shekaru goma ba wajen kai hare-haren bama-baman.

Dubban 'yan gudun hijira ne ke zaune a garin na Biu , inda nan ne ya fi ko ina kwanciyar hankali fiye da sauran sassan jihar Borno da akasar ke karkashin ikon mayakan na Boko Haram.