Kotun Masar ta ba da belin 'yan jaridar Al Jazeera

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An daure 'yan jaridar ne bisa zargin goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi

Wata kotun kasar Masar ta bayar da belin'yan jaridar gidan talabiji din nan na Al Jazeera guda biyu da aka tsare bisa zargin goyon bayan kungiyar 'yan Uwa Musulmi.

An bayar da belin Mohamed Fahmy da Baher Mohamed, wadanda aka tsare fiye da shekara daya.

An zartar musu da hukuncin daurin da ya kai na shekaru goma a kurkuku.

Abokin aikinsu na kasar Australia na cikin wadanda aka yanke wa hukuncin, koda yake an sake shi a farkon watan nan.