Merkel:Akwai yiwuwar sassauci a kan Girka

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Yayinda ta ke magana gabanin taron koli da sauran shugabannin kasashen Tarayyar Turai a birnin Brussels, Mrs Merkel ta ce akan yi sassauci idan ga wanda ya shiga halin matsi-- kuma Jamus a shirye ta ke da ta ta yi wannna sassauci.

Kasar Girka dai ta ce tsaiawta lokacin ceto tan da wa'adin zai kare nan da makonni biyu zai kara durkusar da tattalin arzkinta.

A ranar Laraba ne tattaunawar kasashe masu amfani da kudin Euron ta gaza cimma daidaito.