An soki Jonathan a kan tsagerun Naija Delta

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Jonathan na ci gaba da shan suka daga 'yan kasar

Masu sharhi a kan harkokin siyasar Najeriya sun soki shugaba Goodluck Jonathan saboda kin gargadin tsagerun Naija Delta bayan sun ce idan bai ci zabe ba kasar ba za ta zauna lafiya ba.

A hirar da ya yi da manema labarai ranar Laraba, Mr Jonathan bai yi Alla-wadai da furucin da tsagerun Naija Deltan suka yi ba, duk da tambayar da aka yi masa cewa, "shin mai za ka ce game da furucin da suka yi cewa idan baka ci zabe ba ba za a zauna lafiya ba?"

Dakta Abubakar Kari, wani malamin harkokin siyasa a jami'ar Abuja ya shaida wa BBC cewa matakin da shugaba Jonathan ya dauka na rashin cewa komai a kan batun zai sa 'yan kasar su yi tunanin cewa yana goyon bayan kalaman nasu.

A kwanakin baya ne dai tsagerun Naija Deltan suka ce Najeriya za ta wargaje idan ba a sake zaben Mr Jonathan ba.

'Yan kasar dai na ganin hakan alama ce da ke nuna cewa suna da goyon bayan shugaban kasar, koda yake jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta nesanta kanta daga wadannan kalamai.