Babu batun gwamnatin rikon kwarya a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Shari'a, Bello Adoke

Ministan shari'ar Nigeria, Muhammed Bello Adoke, ya ce kundin tsarin mulkin kasar bai yi tanadi a kan batun gwamnatin rikon kwarya ba.

Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa batun kafa gwamnatin rikon kwarya bakon abu ne a kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 kuma ba a yi tunanin bai wa batun gurbi a cikinsa ba.

Wannan matsayin da Mr Adoke ya fitar, na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan Nigeria ke batun gwamnatin rikon kwarya idan har ba a samu damar gudanar da zabukan kasar ba.

Wasu na zargin Shugaba Goodluck Jonathan da yunkurin yin a fasa kowa ya rasa, ko kuma kafa gwamnatin rikon kwarya, zargin da ya musanta.

Mr Adoke ya kuma bukaci 'yan Nigeria su mayar da hankali a kan abubuwan da za su ciyar da demokuradiyyar kasar gaba.

A watan Maris ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria, inda takarar ta fi zafi tsakanin Mr Jonathan na PDP da Janar Buhari na APC.