Nigeria: An kama 'yan kasashen waje da katinan zabe

Image caption Hukumar zabe na ci gaba da rarraba katinan din-din-din na zabe

Hukumar da ke kula da shige da fice a Nigeria ta ce ta kama wasu matasa kusan 200 'yan kasashen waje dauke da katinan din-din-din na zaben Nigeria.

Shugaban hukumar, David Parradang, ya shaida wa BBC cewa tuni har an koma da wadanda aka kama din zuwa kasashensu na asali.

An kama mutanen ne a jihohin Sakkwato da Katsina da kuma Zamfara.

David Parradang ya ce yawancin matasan da aka kama a wadannan jihohi sun fito ne daga Nijar, da Jamhuriyar Benin da Ghana da kuma Côte d'Ivoir.