Obama zai halarci taro a kan tsaron Intanet

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasashen duniya na nuna damuwa game da tsaron Internet

Shugaban Amurka Barack Obama da kuma shugaban kamfanin Apple Tim Cook na cikin wadanda za su gabatar da jawabai a taron na tsaron intanet a ranar jumu'a.

Taron wanda za a yi a jami'ar Stanford a California zai hada kan jami'an tabbatar da dokoki na wannan fannin.

Ya na kuma zuwa ne bayan Obama ya kaddamar da wani sashe na leken asiri domin duba barazanar tsaron intanet.

Wani babban mamba a hukumar da ke sa ido a kan laifuka a Burtaniya zai bayyana a taron tare da manyan jami'an Microsoft da Facebook da kuma Google.

Fadar White House ta ce Mr. Obama na son a samar da goyan baya ga yunkurin da ake na kiyaye tsaron Intanet da kuma musayar bayanai game da kutsen intanet.

Ana sa ran za a gayyato kamfanoni domin su ba da nasu bahasin game da wannan lamari.