2015: Ban goyi bayan kowa ba — Obasanjo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Obasanjo ya ce nan ba da dadewa zai fitar da matsayarsa

Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce har yanzu bai yanke shawara kan dan takarar da zai mara wa baya a zaben 2015 ba.

Shahararriyar jaridar Financial Times ta ambato Mr Obasanjo yana cewa zai goyi bayan Janar Muhammadu Buhari, yana mai cewa "Idan Buhari ya ci zabe zai gudanar da mulki na daban, ba irin wanda ya yi ba lokacin yana mulkin soji. Shi mutum ne mai hikima. Yana da ilimi, yana da kwarewa. Don haka me ya sa ba zan goyi bayansa ba?"

Sai dai a hirar da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, Mr Obasanjo ya ce har yanzu bai yanke shawara kan wanda zai zaba tsakanin Mr Jonathan da Janar Buhari ba.

Ya kara da cewa nan gaba kadan ne zai yanke shawara kan batun, kuma zai gaya wa duniya matsayarsa.

Mr Obasanjo dai ya sha sukar shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulkinsa.