Ukraine: Putin da Poroshenko sun cimma yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Putin da Poroshenko na Ukraine na shan hannu

Za a soma tattaunawar tsagaita wuta a gabashin Ukraine a ranar Asabar da daddare, tsakanin shugabanin Rasha da na Ukraine, kamar yadda suka sanar inda suke shirin fitar da wani tudun-mun -tsira da ba za a dunga gurmuzu ba.

An cimma yarjejeniyar ce a wata tattaunawa a cikin dare a Minsk.

Shugaban Ukraine, Petro Poroshenko, ya ce bangarorin biyu za su yi musayar fursunoni sannan Ukraine za ta karbi iko da garuruwan kan iyakarta da Rasha.

"Mun cimma matsaya a kan manyan batutuwan," in ji Shugaba Vladmir Putin na Rasha bayan wata tattaunawa da aka shafe lokaci mai tsawo yana yi da Petro Poroshenko na Ukraine da kuma shugabannin Faransa da na Jamus.

Mr Putin ya ce Ukraine za ta janye manyan makamanta sannan 'yan aware masu goyon bayan Rasha za su janye daga wasu fagen daga bisa yarjejeniyar da aka cimma a bara.

'Yan tawayen Ukraine masu goyon bayan Rasha sun amince da yarjejeniyar, koda yake wani kwamandansu 'yan awaren ya ce ba za su ajiye makamansu ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin Faransa da Rasha sun shiga cikin tattaunawar

Tashin hankalin ya yi kamari ne a cikin 'yan makonnin nan, inda 'yan tawayen suka kaddamar da sababbin hare-hare.

Mutane fiye da 5,400 ne suka mutu tun lokacin da aka soma tashin hankalin, a yayin da fararen hula kusan 263 suka mutu cikin kwanaki bakwai.

Ana zargin Rasha da bai wa 'yan tawaye makamai da makamai a gabashin Ukraine amma kuma ta musanta zargin.